
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon Ministan Wutar Lantarkin, Saleh Mamman ya tsere bayan da kotu ta daureshi bisa satar Naira Biliyan 33.8.
Daya daga cikin lauyoyin da suka halarci zaman kotun na yau ne ya bayyana cewa, Saleh Mamman yaki bayyana a gaban kotun da gangan.
Yace kuma tuni kotu tasa a nemo mata shi ruwa a jallo.