Tuesday, May 19
Shadow

Bayani Dalla-dalla: Ji yanda aka kama wani Kwarto a cikin jakar Ghana Must Go a dakin matar aure kamar yanda HISBAH suka sanar

Hukumar HISBAH ta jihar Kebbi ta sanar da kama wani Kwarto a cikin dakin matar aure a boye a cikin jakar Ghana Must Go.

Lamarin ya farune ranar Litinin, 18 ga watan Mayu a unguwar Badariyya dake Birnin Kebbi.

Jama’ar Unguwane suka lura da mutumin ya shiga gidan matar auren inda suka gaggauta sanar da hukuma.

Daraktan HISBAH na jihar, Sirajo Kamba ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yanda daily Trust ta ruwaito.

Yace da jami’an sa suka je gidan suka nemi izinin shiga, matar taki amincewa amma da aka dade ana turjiya sai ta amince.

Aikuwa da bincike yayi tsanani sai ga Kwarto a cikin jakar Ghana Must Go.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Shugaban Darikar Kwankwasiyya Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi Dan wasan Kannywood Ali Artwork Madagwal zuwa Jam'iyyar NNPP

An kamasu duka aka tafi aka fara bincike inda duka suka amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa na soyayya.

Kamba yace za’a gurfanar dasu gaban kotu domin yanke musu hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *