
Sabon Fim din Turanci na Tauraruwar fina-finan Hausa, Fatima Hussain, wadda aka fi sani da Maryam Labarina ta shirya me suna Ammy and Dammy ya jawo cece-kuce sosai.
Tuni wasu suka fara sukar fi din da bayyana cewa, wai ana tabe-tabe tsakanin maza da mata wanda hakan bai dace ba.
Bayan kallon Tallar fim din, Wakilin Hutudole ya lura cewa, tabbas an dan yi tabe-tabe a fim din wanda a al’ada da addinin Arewacin Najeriya hakan bai dace ba.