Mallakar Miji abune da matan aure da yawa ke nema.
A wannan rubutu zamu bayyana muku yanda zaki mallaki mijinki sai yanda kika juyashi.
Abu na farko da zaki yi ki mallaki mijinki shine kyautatawa.
Kyautatawa na da matukar muhimmanci, muna maganar kyautatawa ta fannoni da yawa, wajan bashi abinci, magana,mu’amalar aure da sauransu.
Ki Kyautawa mijinki idan ya kawo muku abinci: Kada ki gaji, a duk sanda mijinki ya kawo abinci ki mai godiya, kamar wannan abinci shine na farko da ya taba kawo muku, wannan zai saka mishi kara sonki da kara kaimi wajan ciyar daku,kuma zai kara masa soyayyarki.
Ki kyautatawa mijinki a yayin da ya zo fita da lokacin dawowa: Idan mijinki yazo fita ki rika masa addu’a, ki masa addu’ar ya jiki “Mijina Allah ya bada sa’a”, “Allah ya dawo mana da kai lafiya” “Allah ya tsareka daga dukkan sharri” Fadi ya ji zai yi tasiri a zuciyarsa, kuma ki dabi’antu da hakan.
Hakanan idan ya dawo, ki masa sannu da zuwa, ki tanadar masa ruwan wanka, da abinci da gurin zama me kyau, ya zamana cewa zai dawo ya tarar da gidanki a tsaftace babu datti,idan kuna da yara, ya zamana suna cikin tsafta, jikinsu da kayansu babu datti, ya dawo su mai oyoyo baya kyamar daukarsu.
Ki rika kyautata abincinki, kin san dai kalar abincin da mijinki yafi son ci, dan haka ki rika kokarin dafashi, ki zuba masa a kwano me kyau da tsafta. Ki rika kokarin bashi abinci a baki,sannan ki rika kokarin bashi labari me dadi a yayin da kike bashi abincin. Idan ya gama cin abinci ki dauke kwanukan ki kuma tsaftace wajan.
Ya zamana cewa, wajan kwanciyarku yana da tsafta, kada ya dawo ya iske gado barkatai daa kaya akai ko baki gyara mashinfidi ba.
Idan kunzo kwanciya, ki kyautata masa, kada ki nuna kosawa.