Wasu gamayyar lauyoyi da suka bayyana kansu a matsayin manyan lauyoyin Arewa sun baiwa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf awanni 48 ya sauke sarki Muhammad Sanusi II daga sarautar sarkin Kano.
Lauyoyin sun fitar da wannan sanarwa ne a Abuja.
Sun kuma bayyana cewa abinda gwamnatin Kano ta yi ya sabawa dokar kundin tsarin mulki da ma al’adar jihar Kano.
Shugaban gamayyar wadannan lauyoyi, Barr. Umar Sadiq Abubakar
Ya bayyana cewa cire Sarki Muhammad Sanusi II da aka yi a karin farko yana bisa ka’ida amma dawo dashi ya sabawa ka’ida kuma hakan na iya kawo rudani a jihar.
Lauyoyin sun zargi gwamna Abba da kin yiwa dokar data hana dawo da sarki Muhammad Sanusi II biyayya.
Sun ce idan Gwamna Abba bai janye matakan da ya dauka na dawo da Sarki Muhammad Sanusi II ba da kuma mayar da Sarki Aminu Ado Bayero kan karagar mulkin Kano ba, zasu dauki matakin shari’a dan kare martabar kotu da mutanen Kano.