
Sultan Abdulrazaq wanda ya gina Gidan shirya fim a unguwarsu ta Dorayi amma aka samu wasu ‘yan unguwarsu suka je gidan Radio suke cewa basu amince ba saboda hakan zai kawo bata tarbiyya.
Sultan yace ba zai yi fada da kowa ba, kawai a samo wanda zai siya gidan zai sayar musu a bashi kudinsa shikenan.
Yace shi dama ya gina gidanne dan samarwa matasan unguwar ayyukan yi.
Ya nuna cikin gidan inda yace babu wani abu na bata tarbiyya a ciki.