
Wannan matashiyar ta dauki hankula a kafafen sada zumunta sosai bayan da ta bayyana inda tace daga garin Bakori na jihar Katsina ta fito.
Tace dai wai kishiyar mahaifiyarta ce ke sata bin maza saboda ita Mahaifiyar ta ta rasu sannan tana sakata Tallah.
Dan hakane ma yasa ta tsere.
Saidai a yanzu Mahaifinta ya bita zuwa Kaduna inda ya bayyana cewa karya take tana da aure ma kuma mahaifiyar ta na nan da rai.
Mahaifin yace ba auren dole yawa diyar tasa ba.