Thursday, July 16
Shadow

Matashiya Mary Habila shekararta 3 tana zaune a karkashina a gidan shakatawa ta watau Guest House>>Inji Ministan Ayyuka David Umahi

Ministan Ayyuka, David Umahi a karin farko yayi magana da ‘yan jarida tun bayan rasuwar Mary Habila a gidansa.

Umahi Yace matashiyar ba mai aikin Tausa bace, kamar yanda aka rika yadawa, malamar Jinyace a Asibitin gwamnatin tarayya.

Yace kuma tana zaune a gidansa ne na shakatawa watau Guest House ita da wata, yace shskararta 3 a karkashinsa.

Yace kwana daya kamin rasuwarta, ta bayyanawa saurayinta cewa hancinta na zubar da Jyni.

Yace a ranar da zata rasu, sun yi waya da saurayinta da dare har tana ce masa bata so ya ajiye wayar amma ya ajiye, daga baya ya kirata, bata dauka ba.

Yace sai da aka balle dakin data rasu a ciki aka tarar da gawarta, sannan kuma an tarar da famfo na zuba, alamar tana shirin yin wanka ne.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Mijin matarnan da akawa kazafin satar yara a Kaduna ya bayar da labari cikin sheshekar kuka

Yace ya bayar da umarnin a yi bincike kan sanadin rasuwarta amma iyayenta sun ce su ba’a haka a al’adarsu.

Yace amma ya rokesu su hakura a yi bincike sannan ya sanar da shugaban ‘yansandan Najeriya game da lamarin.

Ya kara da cewa, masu zarginsa bai kamata a siyasantar da lamarin ba, kawai dan ta rasu a gidansa kuma an tabbatar dakinta a kulle yake ta ciki amma ana zarginsa?

Yace ya baiwa lauyoyinsa umarnin duk masu yada cewa yana da hannu a lamarin a kamasu a makasu kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *