
Hukumar ‘yansandan jihar Jigawa sun tabbatar da rasuwar wani dattijo me shekaru 60 a Duniya a dakin otal bayan sun shiga shi da Budurwarsa me shekaru 20.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mutumin ya nemi a kai masa abinci dakin otal dinsa bayan da suka shiga inda aka kai masa saidai ya rika Numfashi sama-sama wanda hakan yasa aka kira ‘yansanda.
Kakakin ‘Yansandan jihar, SP Shi’isu Adam, yace an kai musu korafin lamarin ranar Talata, July 21, 2026, da misalin karfe 12:50 p.m.
Yace sun garzaya da dattijon zuwa Asibiti inda acan aka tabbatar da ya rasu.
Yace da suka yi bincike sun tarar da wata Budurwa me shekaru 20 da lemu da maganin kara karfin maza a dakin da mutumin ya rasu.
Yace a yanzu suna kan binciken matashiyar me shakeru 20 kuma tana basu hadin kai wajan binciken da ake mata.