
Matashiya Ajebo, Ta fito ta yi Allah ya isa akan Bidiyon ta dake yawo a kafafen sada zumunta.
A wani Bidiyo an jita tana ihu tana kuka tana cewa ba zata sake bin su Otega ba sannan ta daina zuwa Zoo road.
Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda me ake cewa ta je ta bi su Otega sun kwana a Otal ne shine ‘yan uwanta suka bita suke mata hukuncin.
Saidai Ta fito ta karyata inda tace Bidiyon ta yi shine dan Nishadi.
Sannan tace duk wanda suka mata Muguwar fasara akan Bidiyon nata yafe musu ba.
Amma me shafin Kwarmato na Mr. Unknown yace karya take ‘yan gidansu ne suka mata hukunci a Bidiyon da aka ji tana ihu ba da wasa bane kamar yanda take ikirari.