Hukumar kula shigar kaya da fitarsu daga cikin Najeriya, Kwastam ta kama wasu muggan makamai na Naira Biliyan 13.9 a jihar Rivers.
An kama makaman tare da harsasai da kayan sawa na gwanjo da miyagun kwayoyi.
Shugaban hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da yayi ranar Litinin.