Thursday, September 10
Shadow

Wasu da ba’a san ko su wanene ba sun raba matashi Khalil dan Shagamu da Duniya a gidansa dake Kano

Wasu da ba’a san ko su wanene ba sun raba matashi me sharhi a kafafen sada zumunta, Khalil dan Shagamu da Duniya a gidansa dake Kano.

Dan Shagamu kamin barinsa Duniya yayi wani Bidiyo inda yake kira ga Hukumomi cewa ‘yan Izala na farautar rayuwarsa inda aka ji yana kiran sunayen Gwamnan Kano da wasu malamai.

Wannan Bidiyon ya dauki hankula sosai bayan rasuwarsa inda ake ta watsa shi a kafafen sada zumunta.

@sani_abdullahi02

Na dade da sanin Ibrahim Khalil Dan Shagamu a zahiri amma Allah bai hadani da irin bidiyon da yake yi ba sai yanzu bayan ya rash. Allah ya jikan sa ya gafarta masa

♬ original sound – Sani Abdullahi Muaz

Hakanan kungiyar Amnesty international dake ikirarin kare hakkin bil’adama tace ya kamata Gwamnatin tarayya ta dauki matakin hana asarar rayuka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai amaryarsa, A'ishatulhumaira yawon shakatawa, Kasar, Misra/Egypt, kalmar Soyayyar data gaya masa ta dauki hankula sosai

Sannan ta yi Allah wadai da abinda akawa Danshagamu.

Hakanan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumomi da su kamo wadanda suka aikata wannan rashin Imani.

Tuni dai aka kama mutane biyu da ake zargi da yin wannan ta’asa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *