
Musayar kalamai ta barke a gidan Radiyo da talabijin na Brekete Family tsakanin shugaban gidan Radiyon, Ahmad Isa da Aminu Bolo.
Ahmad Isa a karshe ya kira Kwamishinan ‘yansanda na jihar Kaduna inda yace a zo a kama Aminu sannan ya kirashi da banza.
Duk da dai daga baya yace fushi ne yasa ya Kira Bolo da Banza amma ya janye maganar.
Saidai Aminu Bolo yace ba zai yadda da cin fuskar da Ordinary President Ahmad Isa ya masa ba dan har dan garkuwa da mutane ya kirasa.
Yace zai nemi a bi masa hakkinsa.
Sannan a karshe bayan da ‘yansandan suka je gidan Radiyo na Brekete family, aka tattauna.
Basu kama Amini Bolo ba, sun tafi sun barshi.