Zogale na da amfani da yawa, rage Tumbi da kiba na daya daga cikin manyan Amfanin Zogale.
A wani bincike da masana suka gudanar akan mutane 41, an rika basu wani hadin kurkur, Zogale da Curry na tsawon sati 8 inda suka rika hadawa da motsa jiki. Hakan ya taimaka musu sun rage kiba sosai.
Hodar Zogale:
Hakanan bincike ya tabbatar da cewa,hodar ganyen zogale na taimakawa wajan rage kiba, ana iya barbadata kamar yaji ko gishiri a cikin abincin da za’a ci.
Shagin Zogale:
Ana iya hada shayin Zogale da Coffee a rika sha wanda shima yana taimakawa wajan rage kiba. Domin samun amfanin sosai, ana iya fara shan shayin zogale kamin a ci komai da safe.
Ana kuma samun ganyen zogale a wanke.
A zuba a blender a zuba ruwa a markada, idan ba’ da blender a yi amfani da Turmi a daka ana hadawa da ruwa kamar yanda ake surfa wake.
Idan an gama a tace.
Ana iya matsa lemun tsami a cikin wannan ruwa ko a hada da zuma a rika sha kadan-kadan.
Zogale na da sinadaran dake yakar cutar daji watau cancer da ciwon sugar da sauransu.
Yana da kyau a nemi shawarar likita kan amfani da zogale. Hakanan yana da kyau a rika shanshi kadan-kadan saboda duk amfanin abu idan aka yi amfani da shi da yawan da ya wuce kima,za’a iya fuskantar matsala.