Saturday, October 3
Shadow

Kamfanin mai na kasa, NNPCL yace yayi ragin Naira 66 akan kowace lita a gidajen mansa dake fadin Najeriya

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, yayi ragin farashin man fetur na Naira 66 akan kowace lita a gidajen mansa dake Fadin Najeriya.

Kamfanin ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a shafinsa na X

Inda yace yanda za’a samu wannan sauki shine a sauke manhajar sa sannan a yi amfani da ita wajan sayen mai.

Sannan ya kara da cewa wannan sauki zai ci gaba da gudana daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 7 ga watan.

Kamfanin yace Tuni mutane suka fara sayen man akan wannan farashin na ragi.

Karanta Wannan  Namijin Duniya: Wani matashi daga jihar Naija ya auri mata 2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *