
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, yayi ragin farashin man fetur na Naira 66 akan kowace lita a gidajen mansa dake Fadin Najeriya.
Kamfanin ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a shafinsa na X
Inda yace yanda za’a samu wannan sauki shine a sauke manhajar sa sannan a yi amfani da ita wajan sayen mai.
Sannan ya kara da cewa wannan sauki zai ci gaba da gudana daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 7 ga watan.
Kamfanin yace Tuni mutane suka fara sayen man akan wannan farashin na ragi.