Sunday, October 11
Shadow

Kalli Bidiyon: Yanda ‘yan kasuwar Waya na Kano suka fara korar ‘yan kasar China dake sayar da waya a kasuwar

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘Yan kasuwar Waya na Kano sun fara korar ‘yan kasar China dake sayar da waya a kasuwar.

An ga wani Bidiyon dake ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga wani Bahaushe na cewa dan Chinar ya fice musu daga kasuwa.

Ana zargin ‘yan Chinar da zuwa su rika sayar da wayoyi da arha kasa da yanda ‘yan kasuwar ke sayarwa.

A Lagos ma dai Inyamurai sun fito sun nuna rashin amincewar zaman ‘yan kasar China a kasuwarsu inda ska ce a barwa ‘yan Chinar a rika siyo kaya daga kasarsu amma ba su rika zuwa Najeriya suna bude shaguna ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon abin Kunyar da ya faru da gwamnan jihar Adamawa, wanda har sai da jami'in tsaronsa ya fashe da dariya
https://twitter.com/MR__sulaiman2/status/2108562570579783823

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *