
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘Yan kasuwar Waya na Kano sun fara korar ‘yan kasar China dake sayar da waya a kasuwar.
An ga wani Bidiyon dake ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga wani Bahaushe na cewa dan Chinar ya fice musu daga kasuwa.
Ana zargin ‘yan Chinar da zuwa su rika sayar da wayoyi da arha kasa da yanda ‘yan kasuwar ke sayarwa.
A Lagos ma dai Inyamurai sun fito sun nuna rashin amincewar zaman ‘yan kasar China a kasuwarsu inda ska ce a barwa ‘yan Chinar a rika siyo kaya daga kasarsu amma ba su rika zuwa Najeriya suna bude shaguna ba.