Saturday, October 10
Shadow

An kama wasu da kasar Saudiyya ta basu kaya su rabawa Talakawan Najeriya amma suka ki rabawa suka boye

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar ‘Yansandan farin kaya ta DSS sun kama wasu mutane a jihar Taraba saboda boye kayan abinci da kasar Saudiyya ta basu su rabawa talakawa suka ki rabawa.

Rahoton yace kayan abincin sun hada da Farin wake, Shinkafa da sauransu.

An kama wanda ke da dakin ajiyar da kuma wasu mutane 2.

An ga a jikin Buhunan an rubuta ba na sayarwa bane.

DSS dai sun dauki kayan zuwa ofishinsu.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Bayan Rikicin Wike da Sojan Ruwa, shugaba Tinubu yace Sojoji sun cancanchi yabo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *