
Yanda babban jami’in dake kula da tsaro a kamfanin Dangote ya haukace(Sanadiyyar tsananin damuwa) bayan an sallameshi daga aiki sannan daga karshe ya bar duniya ta hanyar hatsari
Labari me ban tausai da Sarkakiya
Wannan baturen sunasa, José Miguel Gaspar Mateus masanin harkar tsaro ne dan Asalin kasar Portugal da kamfanin Dangote ya daukoshi aiki dan ya kula da tsaron duka kamfanonin Dangote
An bashi aikin na tsawon shekaru 3 wanda zai kare a watan Mayu na shekarar 2025.
Saidai bayan karewar kwantirakinsa da kamfanin Dangote, An nemi ya ci gaba da aiki, saidai babu alawus babu bonuses, watau kyautatawa idan yayi kokari, Albashi kawai ake bashi tunda yanzu babu wani kwantiraki, yana aiki ne na wucin gadi, ko jeka na yi ka.
Yana da mata, wadda take cikin rashin lafiya, sannan yaransa 3, biyu daga ciki suna fama da irin cutarnan ta rashin iya yiwa kansu komai sai an musu, shi kadaine ke kula da gidansa ta hanyar kudi da hidimar yau da kullun.
Ya ta neman Kamfanin Dangote su sabunta Kwantirakinsa dan ya ci gaba da aiki da samun kudi yanda ya kamata, amma sunki.
Dan haka ya fara neman wani aikin, sai ya samu aiki a Abuja a wani kamfani inda zasu biyashi albashin da yafi wanda Dangote ke bashi sosai.
Dan hakane ya sanar da Kamfanin Dangote cewa, ya ajiye aiki, sannan ya sanar dasu cewa ya samu aiki a kamfani kaza.
Lauyansa me suna, Fidel Albert, ne yake bayar da wannan labari.
Yace Kamfanin Dangote sun karbi takardar ajiye aikin.
Saidai daga baya an nemeshi cewa Dangote da kansa yana son ganawa dashi.
Yaje inda zasu gana, tsawon awanni kusan 5 Dangote bai zo ba.
Ya tafi aka sake kiransa, ya sake komawa inda zasu gana da Dangote, Dangote bai zo ba.
Can yana zaune sai ga jami’an ‘yansanda sun je wajan suka kamashi suka ce suje ofis, ya tambaya laifin me yayi, suka ce yaje ofis zai ji laifin da ya aikata.
Lauyan Yace an kaishi ofishin ‘yansanda na Zone 2 Zonal Command headquarters dake Onikan, jihar Lagos.
Yace, bayan sun je an bayyana masa cewa, Kamfanin Dangote yace yana zarginsa da cin Amana.
Yace abin ya basu mamaki.
Aka dauki Miguel aka je gidansa aka yi bincike ba’a samu komai ba.
Daga baya ‘yansandan suka ce, idan yana son a sakeshi, sai ya saka hannu a takardar data ce duk abinda ya faru na matsalar tsaro a kamfanin Dangote bayan ya bar aiki ya yadda zai dauki alhakinsa.
Yace saboda ya samu a sakeshi, ya sakawa wannn takarda hannu.
Yace an bayar da belinsa amma an bukaci duk bayan wasu kwanaki ya rika komawa ana ci gaba da bincike.
Da sabon kamfanin da suka daukeshi aiki a Abuja suka ji labarin kamashi, sannan binciken da ake masa ba zai bari ya fara aiki dasu ba, sai suka sanar dashi cewa sun fasa daukarsa aiki.
Anan Miguel ya shiga tsaka mai wuya, bai iya kula da iyalansa.
Dan haka ya koma ya nemi komawa ya ci gaba da aikinsa na Dangote.
Saidai an gaya masa cewa ba’a bukatar aikinsa.
Anan damuwa tai masa yawa, har kwakwalwarsa ta tabu, ya fara zuwa Asibitin mahaukata yana karbar magani.
Daga karshe dai, ‘Yansanda sun fitar da cikakken bayanin binciken da suka yi akan Miguel inda suka ce basu samu wani abu dake nuna cewa yana cin amanar kamfanin Dangote ba, sun nemi wakilan Kamfanin Dangote su je ofishin ‘yansandan dan a karkare magana amma suka ki zuwa.
A karshe dai suka sallami Miguel suka rufe case din, ya koma kasarsa.
Lauyan Miguel yaci gaba da cewa, Bayan da ya koma kasarsa.
Wata rana ya dauki Mashin dinsa irin na Sports dinnan ya fita, suka yi taho mu gama da wata mota, ya rasu.
Lauyan Yace a ranar da zai yi hadarin sun gaisa dashi da safe.
Yace kuma matarsa tace ya dauki mashin din ne ya fita dan ya manta da damuwar da yake ciki.
Yace kamin rasuwar Miguel, sun fara tattara bayanai dan kai Dangote kara kotu a nema masa hakkinsa.
Yace amma yanzu duk da ya rasu, zasu kai wannan kara amma yanzu matar Miguel ce zata shigar da karar.
Sannan lauyan yace shi yana ga wannan rasuwa ta Miguel ba ta Allah da Annabi bace, akwai wata makarkashiya a ciki.