Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ta baiwa membobinta umarni a jihohin da basu fara aiwatar da mafi karancin kasafin kudin dubu 70 ba su shiga yajin aikin sai abinda hali yayi daga ranar 1 ga watan Disamba.
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da suka yi a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake duba wasu tsare-tsaren ta wanda yace suke cutar da mutane inda yace hakan ya jefa mutane a matsin rayuwa da kunci.
Shugaban kungiyar Kwadagon yace sun kafa kwamiti na musamman da zai duba da kulawa da yanayin aiwatar da mafi karancin albashin da wayar da kan ma’aikata su tashi tsaye su nemi hakkinsu.