
Hukumar zabe me zaman Kanta, INEC ta musanta Rahotan dake cewa wai ta cire Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi daga jerin ‘yan takarar shugaban kasa.
INEC tace wannan Rahotan bashi da tushe ballantana makama.
Me magana da yawun INEC, Mohammed Kudu Harun me ya bayyana hakan.
Yace zuwa yanzu basu karbi kwafin Hukuncin Kotun ba wanda sai dashine zasu samu hujjar cire sunan Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi daga jerin ‘yan takarar.