Saturday, November 7
Shadow

Ana zargin Ma’aikaciyar Bankin Ja’iz ta kwashe kudaden Kwastomomi Har Naira Miliyan 104

Ana zargin Ma’aikaciyar Banki Habiba Abdulrahman da yin sama da fadi da kudaden Kwastomomi har Naira Miliyan 104

Lamarin ya farune a bankin Ja’iz Dake jihar Filato

Inda Kwastomomin suka bata kudadensu da tunanin ta saka musu a asusun bankunansu ashe bata saka ba.

Ana zargin ta yi amfani da Asusun bankin Mijinta da na kanwarta inda ta rika tura kudin a ciki.

Tuni dai bankin suka koreta daga aiki a farkon wannan shekarar da muke ciki inda kuma aka mikata wajan ‘yansanda.

Bayan Bincike ‘Yansanda sun gano wasu takardun bankin a gidanta sannan ta amsa laifinta na cewa ta kwashi kudaden Kwastomomin wanda dama can bata sakasu a asusun bankunan Kwastomomin ba.

Karanta Wannan  Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Tace ta yi amfani da kudadenne wajan yin harkar hakar ma’adanai amma babu shaidar hakan.

Saidai Kwastomomin da abin ya shafa sun fito zàngà-zàngà inda suke cewa, a basu kudinsu.

Jaridar Daily Trust ta nemi jin ta bakin Lauyan Bankin, Inda yace musu Magana tana kotu dan haka yayi mamakin ganin Kwastomomin suna Zàngà-zàngà.

Yace kuma da ita suka yi hulda ba da banki ba, dan har gida suka rika binta suna bata kudi wanda ba haka ake saka kudi a banki ba.

Binciken Daily Trust ya bayyana cewa, Habiba Tana walwalarta a gari duk da wannan zargi da ake mata.

Binciken yace da farko da aka taso da maganar, ‘yansanda sun kamata amma bayan sati biyu tana tsare, an bayar da belinta bisa hujjar rashin lafiya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda aka hana wata daliba rubuta jarabawar JAMB saboda ta saka Hijabi

Daily Trust ta nemi jin ta bakin Habiba inda tace nan gaba zata bayyana nata bangaren abinda ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *