Monday, December 16
Shadow

BATUN ŹÀNĢA-ŹÀNĢA: Minista Na So Jama’a Su Ķara Haƙuri Ďomin Tinubu Yana Ķoƙarin Ŕage Matsi

BATUN ŹÀNĢA-ŹÀNĢA: Minista Na So Jama’a Su Ķara Haƙuri Ďomin Tinubu Yana Ķoƙarin Ŕage Matsi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman matasa masu shirin zanga-zanga, da su yi haƙuri.

A halin yanzu wasu ‘yan Nijeriya na ta yin shelar cewa za su yi zanga-zangar lumana a ƙarshen wannan watan domin bayyana ɓacin ran su kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta a yau.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Asabar, ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta ɗauki wasu muhimman matakai domin magance matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

Ya ce: “Akwai mataki na farko da gwamnati ta ɗauka na a samu a raba kayan abinci ga al’ummar Nijeriya. An kai shinkafa jihohi duka ga baki ɗaya talatin da shida da kuma yankin Abuja.”

Ya ƙara da cewa, “Akwai wani shiri da ake yi na CNG, ma’ana wannan harka na iskar gas wanda duk motocin da za su yi aiki za su yi aiki da wannan na’ura, wato na iskar gas, ma’ana misali idan kana kashe naira goma wajen sufuri yanzu kuɗin ka zai dawo ƙasa ma da naira huɗu. Ka ga an sake samun cigaba.

Karanta Wannan  RANAR HAUSA: Dole Mu Tuna Da Marigayi Sheik Abubakar Mahmoud Gumi A Wannan Rana

“In ka lura da abin da ake yi kamar na bututun gas na AKK wanda kwanakin baya an je Kaduna an sake duba shi, ya kai kusan wato kashi casa’in da biyar da gamawa. Abu ne da aka fara tun waccan gwamnatin da ta shuɗe.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kuma ya tsaya tsayin daka lallai a samu a gama wannan shiri saboda idan aka yi shi za a samu sauƙi sosai.

“Duk kamfanonin da aka rurrufe saboda matsalar wutar lantarki da ɗimbin al’umma da suka rasa ayyukan su saboda rufe kamfanunnuka idan Allah ya yarda za su dawo.”

Ministan ya yi nuni da cewa Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da Shirin Lamunin Ɗalibai don ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi su samu damar zuwa makaranta.

Karanta Wannan  Sunaye masu dadi na maza da mata

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma ƙaddamar da harkar wato abin da ake ce ma Student Loan, wato bashi saboda a yi makaranta. Yana takaicin cewa bai kamata a ce wani yaro bai iya zuwa makaranta ba saboda iyayen sa ba su da kuɗin biya masa makaranta.

“Yanzu duk wani wanda ya iya cin jarabawa, duk wani yaro ɗan Nijeriya, cikakken ɗan Nijeriya da ya iya cin jarabawa, zai iya zuwa ya amfana a biya masa bashi mai sauƙi cikin rahusa ya biya kuɗin makaranta, ba ma kawai a biya kuɗin makaranta ba, ya samu kuɗin da kuma zai iya ɓatarwa har ya gama karatun sa.”

Dangane da wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta duk da alƙawurran da Shugaba Tinubu ya yi na kawo sauƙin rayuwa, Idris ya ce: “Lallai gwamnati ta yarda cewa akwai wannan matsatsi. Abin da ya bambanta gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatoci da yawa shi ne idan akwai matsala akan amsa a ce lallai akwai matsala a wuri kaza amma kuma ga abin da mu ke yi na a samo maslaha.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin a fara sayar da man fetur akan sama da Naira Dubu daya kowace lita

“A yanzu maganar da ake yi a harkar tsaro abin da muke ciki misali shekara ɗaya baya, ko shekara biyu baya, ai ka ga abin ba haka ba ne.

“Mu na fata a haɗa ƙarfi da ƙarfe, su mutanen ƙasa su ba gwamnati goyon baya domin a kawo ƙarshen wannan al’amari.

“Saboda haka a ƙara yin haƙuri, kiran da gwamnati ke yi kenan. A ƙara yi wa gwamnati haƙuri, idan Allah ya yarda a hankali a hankali za a kawo ƙarshen wannan al’amari.”

Ministan ya ce akwai tanadi da gwamnati ta yi wa manoma inda Babban Bankin Nijeriya (CBN), ta hanyar Ma’aikatar Aikin Gona, ya raba taki buhu miliyan dubu ɗari ɗaya da hamsin ga manoma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *