Amosanin Ido illace wadda ke bukatar kulawa saboda yanda lamarin kan taba lafiyar idon mutum.
Likitoci na amfani da hanyoyin bayar da maganin digawa, bayar da maganin sha ko kuma yin aiki ga masu fama da amosanin ido.
Yana da kyau a samu likitan ido ya duba dan bada shawara irin ta kwararru ga me fama da matsalar amosanin ido.
Akwai hanyoyin gargajiya da ake amfani dasu wajan magance matsalar amosanin ido:
Shan Dinya: Masana sunce Dinya tana taimakawa masu fama da matsalar amosanin ido da sauran matsalolin ido.
Gashin Danyar Masara: Eh Gashin danyar masara dai da ake cirewa a yadda yana da matukar amfani ga masu ciwon ido musamman ma Amosanin ido, yana kuma taimakawa masu hawan jini, yana kashe abubuwan dake kawo tsufan jiki da wuri, yana kuma taimakawa masu ciwon suga sosai, yana taimakawa lafiyar zuciya, yana taimakawa masu fama da matsalar mafutsara, yana maganin kumburin jiki. Ana iya cin gashin masarar ko kuma a yi shayin sa a rika sha.
Hakanan Man Kifi shima yana maganin matsalar ido irin ta Glaucoma da sauransu.
Hakanan Wiwi itama tana maganin matsalar ido, amma ita maganin da take yi na dan lokacine.
Allah ne mafi sani.
Allah ya karemu da lafiya.