INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRAJI’UN
Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri.
Humaira ta bayyana rasuwar a shafinta na Instagram inda ta nemi al’ummar musulmi da su sanya ta cikin addu’a Allah Ya gafarta mata tare da sauran al’ummar Annabi (S.A.W) da suka riga mu gidan gaskiya.
Za a yi mata sallar Jana’iza a gobe da safe, a birnin Maiduguri na Jihar Borno.