Thursday, October 3
Shadow

Gyaran gashi da ruwan shinkafa

Mutanen kasar China da Japan sun dade suna amfani da ruwan shinkafa wajan kara tsawon gashi da kuma hanashi yin furfura.

Hakanan kuma a wani kaulin,ruwan Shinkafa na hana gashin mumurdewa da hadewa da juna.

Hakanan kuma ruwan shinkafa na karawa gashin kai sheki.

Matan wani kauye a China me suna, Huangluo na daga matan da suka fi kowane mata tsawon gashi a Duniya inda aka ruwaito cewa gashin kansu hana kai tsawon kafa 6.

Sannan kuma gashin kansu yawanci bai fara yin furfura sai sun kai kusa da shekaru 80 a Duniya.

Wadannan mata sun bayyana cewa sirrinsu shine wanke gashin kansu da suke yi da ruwan shinkafa.

YANDA ZA’A SAMU RUWAN SHINKAFA DAN GYARAN GASHI

Akwai hanyoyi 3 da ake samun ruwan shinkafa dan gyara gashi dashi.

Karanta Wannan  Gyaran gashi da wiwi

Danyar Shinkafa: Ana samun danyar Shinkafa rabin kofi.

Sai a Daurayeta.

A zuba a mazubi ko kwano.

A zuba ruwa kofi 2 ko uku.

A bari ta yi mintuna 30 zuwa Awa 1.

Sai a tace a yi amfani da ruwan.

Dafaffar Shinkafa: Ana amfani da ruwan dafaffar shinkafa wanda aka tace wajan gyaran gashi.

Shima yana bada sakamako me kyau sosai.

Giyar Shinkafa: Kamin mu fara bayani, a yi hattara, wannan abinda zamu fada yanda ake hada giyar shinkaface.

Kuma kowane musulmi ya sani shan giya haramunne dan haka idan aka hada kada a yi gigin sha ko a ajiye inda yaro wanda bai da hankali zai iya gani ya sha.

Mafi a’ala shine kada a hada da yawa, a hada iya wadda za’a yi amfani da ita, idan kuma an tashi sake yi, sai a sake hadawa maimakon a hada da yawa a ajiye.

Karanta Wannan  Hadin tsawon gashi

Dalilin da yasa zamu koyar da yin giyar shinkafa shine a iya binciken mu yin amfani da giya dan gyaran gashi ba haramun bane a muaulunci, Allah ne mafi sani.

YANDA ZAKU HADA GIYAR SHINKAFA

Ana samun ruwan dafaffiyar shinkafa a ajiye shi ya kwana biyu, idan ana da firjin ana iya sakawa ciki,idan babu duka ba matsala bane ana iya samun wani guri inda yara ba zasu iya daukowa ba a ajiye.

Hakanan ita kanta shinkafar wadda aka dafa ta kwana, ana ajiye ta ta kwana biyu a rufe, idan ta kwana biyu za’a ga ta fara tsami ko wari da fitar da wani farin ruwa, to a wannan lokaci ta zama giya.

Za’a iya juyata da kyau dan gaba daya ta zama ruwa dan a ji dadin amfani da ita.

Karanta Wannan  Gyaran gashi da man kadanya

Munce kwana biyu ne saboda shine mafi karanci, amma yawan dadewar ruwan shinkafar ko shinkafar a ajiye yana karawa giyar karfi. Ma’an za’a iya ajiyewa fiye da kwana biyu.

Yanda ake amfani da giyar shinkafa, kamar dai yanda ake amfani da ruwan shinkafar ne. Wasu ma sunce giyar shinkafar tafi ruwan shinkafar amfani sosai.

Ana fara wanke dai da Shampoo.

Sai a dauraye da ruwa.

Daga nan sai a zuba ruwan shinkafar a wanke kai dashi sosai, ya shiga ko ina a cikin kan.

Sai a barshi zuwa mintuna 20.

Sannan sai a wanke da ruwan dumi.

Ana iya yi duk sanda za’a wanke kai, ko sau biyu a sati ko sau daya a sati, ya danganta yanda ba zai takura rayuwar mutum ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *