Ma’aikacin dake aiki a filin jirgin sama na malam Aminu Kano dake jihar Kano, Auwal Dankode wanda ya tsinci dala $10,000 kwatancin sama da Naira Miliyan 15 ya mayar da ita ga maisu ya samu karin girma.
Auwal ya samu karin girma da kyautar kudi sannan an bashi aikin jakadar hukumar NAHCO da yakewa aiki.
Shugaban hukumar, Mr. Indranil Gupta ne ya bayyana haka inda yace auwal ya nuna kwarewa da jajircewa da gaskiya wajan aikinsa inda ya karfafeshi cewa ya ci gaba da wannan aiki.
Auwal dai ya tsinci kudinne yayin da yake aikin share jirgin saman Egypt Air, kuma nan take ya mika kudin ga shugabansa.