Wednesday, October 9
Shadow

Gwamatin Tarayya Ta Sanar Da Shirinta Na Zuba Jarin Dalar Amurka Biliyan 4.8 a Fannin Kiwon LafiyaNajeriya

Gwamatin Tarayya Ta Sanar Da Shirinta Na Zuba Jarin Dalar Amurka Biliyan 4.8 a Fannin Kiwon LafiyaNajeriya

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayinda yake karin haske kan sauye-sauyen da gwamnatin ta yi a fannin kiwon lafiya wanda a cewarsa, zai lashe sama da dala biliyan 4.8 wajen zuba jari duk a yunkurin gwamnati na ganin an farfado da ingancin kiwon lafiya a Najeriya tare da magance Kalubalen da ya jima yana addabar bangaren kiwon lafiyar

Shettima, ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da rukunin asibitocin Sahad a birnin Abuja,

“Gwamnatin mu ta kuma Kaddamar da gyare-gyare a kan bangarori huɗu masu mahimmanci wanda suka haɗa: sauya tsarin kula da kiwon lafiya, samar da ingatattun bangarorin binciken lafiya, buɗe Sabbin Cibiyoyin , da ƙarfafa sashin riga-kafi ga kamuwa da cututtuka.

Karanta Wannan  Cin yaji ga mai ciki

Shettima ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su shigo wannan tsarin saboda muhimmancinsu ga cimma burin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Najeriya.

Kashim, ya kuma yaba wa mammallakin Kamfanin Sahad Group of Companies, Alhaji Ibrahim Mijinyawa, bisa namijin kokarin da yake yi na samar da ingantaccen kiwon lafiya.

Asibitocin Sahad din dai sun kunshi dakuna masu gadaje 200 da kuma kayan aikin kula da lafiya na zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *