Monday, December 16
Shadow

An kama Boka bayan da ya baiwa wani mutum maganin bindiga kuma aka yi gwajin harba bindigar saidai maganin bai yi aiki ba, Mutumin ya mutu

Wani boka me suna Timothy Dauda dan kimanin shekaru 19 a jihar Edo da yayi ikirarin yana da maganin Bindiga ya shiga hannu.

An kamashine bayan da ya gwada maganin Bindigar akan wani amma maganin bai yi amfani ba,Bindigar ta kamashi ya mutu.

Lamarin ya farune a yankin Onumu dake karamar hukumar Àkókò-Edo A jihar ta Edo

Kakakin ‘yansandan jihar SP Moses Joel Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargi zai fuskanci hukunci.

Karanta Wannan  Jihar Gombe ta kulla yarjejeniya da kamfanin kasar China dan samarwa da kanta wutar Lantarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *