Saturday, December 21
Shadow

Idan ‘yan kasuwa suka ki sayen man fetur dina zan fitar dashi kasar waje na sayar>>Dangote

Hukumomi a matatar man Dangote sun bayyana cewa idan ‘yan kasuwar man fetur din suka ki sayen mansu,zasu fitar da man zuwa kasashen waje su sayar.

Mataimakin shugaban bangaren Oil and Gas na matatar, Devakumar Edwin ya bayyana hakan a shirin Berekete Family.

Yace ‘yan kasuwar sun musu haka akan Gas da man jirgin sama suka yi saye a hannunsu suka rika zuwa kasashen waje suna siyowa, yace dole saidai sayar da gas din da man jirgin saman suka rika yi zuwa kasashen waje.

Yace idan ‘yan kasuwar suka musu haka akan man fetur da suka fara samarwa shima zasu fitar dashi zuwa kasashen waje su sayar.

Karanta Wannan  Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *