A Zaman Da Muka Yi Da Ku Babu Wata Yarjejeniya Dake Da Alaka Da Cewa Ba Za A Kara Farashin Man Fetur Ba, Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Kungiyar Kwadago
Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, inda ya kara da cewa a dukkan zaman da aka yi tsakanin bangarorin biyu a kwanakin baya babu wanda ba a gabansa aka yi ba, kuma ba a yi maganar farashin mai ba.
Malam Abdulaziz Abdulaziz ya yi martanin ne a shafinsa na X (twitter).