Dan kwallon Najeriya, Ademola Lookman ya shiga jerin ‘yan wasan da zasu iya lashe kyautar Ballon D’ Or ta shekarar 2014.
Lookman ya shiga jerin manyan ‘yan kwallon Duniya irin su Bellingham, Kylian Mbappe da Vinicius Jr wanda ke gaba-gaba wajan lashe kyautar.
Dan wasan yayi kokari sosai a gasar Serie A inda ya ciwa kungiyarsa ta Atalanta kwallaye 3 a wasan da suka buga da Bayer Leverkusen a gasar Europa.
Hakanan a gasar AFCON,ya ciwa Najeriya kwallaye 3.
A baya dai an yi rade-radin zai koma kungiyoyin Arsenal da PSG saidai a karshe be bar kungiyar tasa ba.