Shugaban gamayyar kamfanonin Dangote wanda ke da matatar mai ta Dangote Refinery ya ce matatar ta shiya tsaf domin fara sayar da tataccen man fétur da disel har ma da kanazir ga gidajen man kasar.
Alhaji Aliko Dangote ya shaidawa BBC matatar tana iya samar da fiye da man da ake bukata a kasar.
”Inda mu ke ciki yanzu mun soma yin mai, muna jiran su zo su soma karba saboda abinda aka yi a sabon tsari shi ne za su ba mu man fetur da za mu sarafa wanda za mu basu”, in ji shi.
Ya kara da cewa kamfanin mai na kasa NNPCL ne ke da alhakin saka farashin litar man da matatar tasa za ta fitar:
”Wajan saka kudin mai ba a hannunmu yakeba, a hanun NNPC yake ,kawai abinda zan iya tabbatar cewa a yanzu muna da man fetur da Kananzir da disel, duk wadannan wadanda za mu iya ba wa Najeriya fiye da abinda za ta iya sha, saboda haka gidajen sayar da man fetur a Najeriya nan gaba za su shiga aiki domin muna da fiye da abinda kasuwar take bukata”
”Ai ka san wannan batun sa farashin mai, aiki ne na gwamnati idan ya zo ga zance man fetur, na disel shi wannan daban ne. Shi na disel idan ka duba lokacin da mu ka soma, da a can naira dubu 1,700 amma sai da mu ka sayarda shi kasa da naira dubu 1.Yanzu ya koma dubu 1, 200 saboda farashin dala amma ka ga shi wannan ba bu wani da za ka je ka gani a layi, ana nema a saya” in ji sji
Sai dai Dangote ya ce abu ne mai wuya farashin man fetur ya sako ko da matatarsa ta fara sayar da man fetur
”Shi a yanzu idan ka duba za ka ga cewa wannan magana ce ta gwamnati, zance ya sauka zai yi wahala a haka, saboda idan ka riga ka duba a yau fetur, kamar a Saudiyya, da a can mai din kusan komai kyauta ake ba da wa amma idan ka je yanzu za ka ga cewa riyal 2 .35 zuwa 38. To wannan ma kansa ka yi shi akan dubu 1,600 ya fi naira dubu.
Ya kuma ce suna kan tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da saka farashin da zai sayar wa dilalan man fetur watau IPMAN
”Ai kan san sabon tsarin da aka yi yanzu idan an hako man za a sayar mu na da shi a naira, mu kuma mu dauki fetur mu bada shi a naira, a yanzu ana cikin tattaunawa, idan an gama tattaunawar din na tabbatar duka za a sanar da ku me ake ciki”