Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni bai bar gidansa dake Abuja dan komawa jiharsa ba duk da kisan da ‘yan Boko Haram sukawa mutane da yawa a jihar tasa.
Hakan yasa yake ta shan suka daga ciki da wajen jihar.
Dama dai tun a baya akwai rahotannin dake bayyana cewa,Gwamnan daga Abuja yake gudanar da mulkin jihar wanda hakan ya jawo suka gareshi.
Kingiyar ISWAP tace itace ke da alhakin kai harin inda tace ta kai harinne bayan da mutanen garin suka baiwa sojoji bayanan sirri wanda suka kai ga kashe membobinta.
Mutane da yawa dai daga jihar sun rika amfani da kafafen sada zumunta domin bayyana rashin jin dadinsu kan halin da gwamnan ya nuna.