Saturday, December 21
Shadow

Buhari Ya Aika Da Tawaga Zuwa Katsina Domin Yin Ta’aziyyar Dada ‘Yar’Adau A Madadinsa

Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari, ya aika da tawaga mai ƙarfi karkashin jagorancin tsohon ministan sufurin jiragen sama Sen. Hadi Sirika, domin gabatar da ta’aziyar Hajia Dada, mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua a garin Katsina.

Tawagar ta kunshi tsohon ministan Shari’a Abubakar Malami SAN, da Sanata Hadi Sirika da kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Daura da wasu tsofaffin muƙarraban gwamnatinsa.

A cewar, Hadi Sirika, Buhari ya kaɗu a lokacin da sakon rasuwar Haj. Dada ya riske shi a kasar Ingila.

Daga Comr Nura Siniya

Karanta Wannan  Mutane 243,000 sun daina biyan kudin talabijin ta DSTV a Najeriya saboda tsadar rayuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *