Aliko Dangote ya koka da cewa, ‘yan kasuwar man fetur sun koka da cewa man fetur dinsa yayi arha da yawa.
Dangote ya bayyana hakane ta bakin wakilin kamfaninsa,me suna Devakumar Edwin.
Ya kara da cewa,tuni ‘yan kasuwar suka aikawa da shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu korafi akan wannan lamari.
Yace da kyar suke samun suna sayar da tankar Gas 29 saboda ‘yan kasuwar basa son saye, yace dan haka dole suke fitar da sauran zuwa kasashen waje.
Kamfanin dai na Dangote ya rage farashi daga Naira 1200 zuwa Naira 1000 zuwa Naira 900 akan kowace lita.