Wannan matashiyar daga jihar Borno ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta daga jihar Borno.
A wani faifan bidiyonta daya watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga matashiyar tana kokawa da irin illar da ambaliyar ruwan ta musu.
Hakan yawa mutane da yawa suka sha Alwashin tallafa mata inda tuni wasu suka bayyana cewa sun fara aika mata da tallafin kudi.
Ambaliyar ruwan dai ta jefa mutane cikin halin rashin tabbas inda wasu dole suka bar gidajensu suka koma kodai wajan ‘yan uwa ko suka shiga halin rayuwar rashin tabbas.