Sojan Najeriya, M.S Adamu wanda ake zargin ya daure karamin soja, Abbas na shan Allah wadai da kiran a hukuntashi saboda hukuncin da yawa Abbas yayi tsauri.
Matar Abbas ce dai ta je kafar Berekete Family inda ta bayyana cewa an daure mijinta bayan da yaje Sallah ya dawo ba tare da neman izini ba.
Sannan ogansa na magana shima yana magana.
An daureshi dai bayan da kansa ya daku ya rika fitar da Jini wanda hakan yasa kwakwalwarsa ta tabu ya samu tabin hankali.
Daga baya dai an kaishi Asibiti aka masa magani.