Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu, Paul Mashatile ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da jawabi.
Bidiyon faruwar lamarin ya yadu a kafafen sada zumunta sosai.
Lamarin ya farune a garin Tzaneen dake Limpopo na kasar.
Rahotanni sunce mataimakin shugaban kasar ya fadi ne saboda tsananin zafi da ake yi.
Ba dai a kaishi Asibiti ba dan lamarin bai yi muni ba.