Albasa na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajan gyaran gashi da sawa yayi tsawo da kuma kara masa kwari.
Yanda ake hadin shine ana samun Albasa a bare.
Sai a yayyankata kanana-kanana a saka a abin markade a markada ko a daka.
A tabbatar ta yi ruwa, sai a tace.
Ana hada ruwan da man kwakwa a rika shafawa akai ko a hada da man shampoo da ake dashi a gida, yana taimakawa sosai wajan gyaran gashi da kara mai tsawo.
Ana hada wannan ruwa na Albasa da ruwan lemun tsami musamman dan a batar da warin Albasar.
Hakanan ruwan Albasan yana taimakawa wajan hana gashi fara furfura da wuri.
A wani kaulin ma yana taimakawa wajan boye furfura.
Ana iya hadashi ruwan lemun tsami a shafa akai na tsawon mintuna 30 sannan a wanke.
Dan samun sakamako, a yi hakan sau 2 a sati.