Thursday, October 3
Shadow

Gyaran gashi da ganyen magarya

Domin yin gyaran gashi da ganyen Magarya,ga bayani a kasa kamar haka:

A samo ganyen danyen lalle ko na magarya.

A Samo Garin Hulba ko tsaba.

A sako man zaitun

A samo Man Ridi.

A Samo Man Habbatussauda.

A samo Man Kwakwa.

YADDA AKE HADAWA

Ana hada ganyen lalle, Ko na magarya, da garin Hulba a waje daya a zuba a tukunya a tafasa a sauke ya huce, kada a bari ya huce gaba daya,yayi dumi yanda za’a iya wanke kai dashi.

Kanki kuma,zaki hada wadancan mayukan da muka ce a samu a sama sai ku shafa sosai akan ya shiga ko ina.

Sai ki sa a gashinki a Leda ki daure zuwa mintuna 15.

Bayan nan sai ki yi amfani da ruwan hulba da ganyen lalle ko na magarya dincan da kika dafa ki wanke kan. Ki barshi ya bushe.

Karanta Wannan  Gyaran gashi da kwai

Sannan zaki sake shafa masa mai.

Sai ki je a miki kitso.

Za’a iya yi sau 2 a wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *