Wata karuwa ta kashe abokin lalatarta bayan da ya dauketa ya kai gidansa.
Lamarin ya farune a jihar Legas a unguwar Jakande.
Mutumin me suna Okafor ya dauki karuwar, Joy Kelvin ya kai gidansa inda a canne ta caka masa wuka ya mutu.
Lamarin ya faru a daren 6 ga watan October inda a wayewar gari watau ranar 7 ga wata sai abokin mamacin ya kira ‘yansanda.
An garzaya da Okafor zuwa Asibitin Marina inda a canne suka tabbatar ya mutu.
Tuni dai aka kama Joy inda shi kuma aka kai gawarsa zuwa mutuware yayin da aka ci gaba da neman ‘yan uwansa.