Wani magidanci ya sayar da dansa me watanni 11 kacal a Duniya inda yayi amfani da kudin wajan buga caca.
Ya sayar da dan nasu ne ba tare da sanin matarsa ba.
Lamarin ya farune a yankin Tangerang, West Jakarta na kasar Indonesia.
Matarsa ta koma gida bata ga dan nasu ba inda ta tambayeshi, da ya fara mata kame-kame amma daga baya ya fito ya gaya mata gaskiya.
Tuni ‘yansandan ‘yankin su suka kamashi.
Ya dai sayar da danne akan farashin £730 kuma tuni suma wanda suka sayi dan aka kamasu.