Wednesday, December 11
Shadow

Magidanci ya sayar da Dansa me watanni 11 kacal a Duniya ya buga caca da kudin

Wani magidanci ya sayar da dansa me watanni 11 kacal a Duniya inda yayi amfani da kudin wajan buga caca.

Ya sayar da dan nasu ne ba tare da sanin matarsa ba.

Lamarin ya farune a yankin Tangerang, West Jakarta na kasar Indonesia.

Matarsa ta koma gida bata ga dan nasu ba inda ta tambayeshi, da ya fara mata kame-kame amma daga baya ya fito ya gaya mata gaskiya.

Tuni ‘yansandan ‘yankin su suka kamashi.

Ya dai sayar da danne akan farashin £730 kuma tuni suma wanda suka sayi dan aka kamasu.

Karanta Wannan  Ji yanda wani tela yawa wata mata karyar cewa yana da cutar Kanjamau bayan data tsareshi a gidanta ta matsa mai sai yayi làlàtà da ita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *