Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu ta IPMAN ta yi barazanar daina aiki idan kamfanin mai na kasa,NNPCL bai dakatar da karin kudin man fetur din da yayi ba.
Gidajen man fetur mallakin kamfanin man fetur na kasa,NNPCL na fadin Najeriya sun kara farashin man fetur dinsu inda aka rika sayarwa daga Naira 998 zuwa Naira 1070.
Hakan yasa kungiyar IPMAN ta bakin wakilinta, Chinedu Ukadike tace basu yi na’am da wannan mataki na karin kudin man fetur din ba inda tace zasu dakatar da aiki muddin ba’a janye wannan kari ba.
Kungiyar dai ta IPMAN ce ke da kaso 70 cikin 100 na gidajen man dake fadin Najeriya.
Chinedu Ukadike ya kara da cewa su idan zasu saida nasu man a matsayin ‘yan kasuwa zai iya kaiwa naira 1,200 kan kowace lita.
Dan haka yace zasu kauracewa man fetur din na kamfanin NNPCL.