Me fafutukar kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho ya kai takardar neman goyon bayan kafa kasar Yarbawan zuwa ga ofishin kasar Ingila dake Landan.
Sunday Igboho yayi kokarin ganin kafa kasar ta Oduduwa amma bai cimma nasara ba inda a karshe sai da ya tsere daga Najeriya saboda yanda jami’an tsaro ke nemansa ruwa a jallo.