Wakilin kamfanin Dangote, Devakumar V. G. Edwin ya bayyana cewa, mafi yawan ‘yan kasuwar man fetur na Najeriya basa sayen man fetur din daga matatarsu.
Ya bayyana hakane a wata hira ta musamman da aka yi dashi inda yace kaso 95 na ‘yan kasuwar man fetur din basa saye daga wajensu.
Yace hakan yasa dole suke fitar da man fetur din nasu zuwa wasu kasashe dan sayarwa.