Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Bindigar sun shiga unguwar Waliyi Estate dake dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina ranar October 16, 2024 inda suka yi garkuwa da wata matashiya.
Kamin sace matashiyar sai da suka yi harbin kan mai uwa da wabi.
Rahoto ya bayyana cewa a baya sun kashe mahaifan matashiyar inda kuma yanzu suka dawo dan yin garkuwa da ita.