Shugabar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM), Hajiya Hajara Mohammed ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 23 da kuma kujerun kansiloli 255 na jihar.
A baya Gwamnan Jihar kaduna Mal Uba sani Yasha alawashin lashe Zaben Kananan hukumomin.